ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa rikicin ya yadu zuwa birnin Johannesburg daga arewacin kasar, inda wasu matasa suka yi ta wawason dukiyoyin mutane, wasu kuma suka faffasa shaguna suna ta satar kayakin mutane.
Jami’an tsaro na farin kaya da ‘yansanda sun bada sanarwan cewa an kama mutane akalla 62 a jiya Lahadi.
An fara rigimar nuna fushin kama Zuma ne a mahaifarsa wato yankin KwaZulu-Natal sannan a hankali rikicin ya watsu zuwa wasu jihohin.
Jocop Zuma dai shi ne tsohon shugaban kasar Afirka ta kudu da aka taba daurewa tun bayan da kasar ta sami ‘yenci daga hannun turawa masu nuna wariyar launin fata shekaru 27 da suka gabata.
Banda haka Jocop Zuma ya na da wata sharia ta cin hanci da rashawa da take jiransa.
342/